Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Kenya Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanga A Birnin Nairobi


‘Yan sanda a Nairobi, babban birnin Kenya sun harba barkonan tsohuwa kan masu zanga-zanga da zaman durshe a gaban ofishin gwamnati
‘Yan sanda a Nairobi, babban birnin Kenya sun harba barkonan tsohuwa kan masu zanga-zanga da zaman durshe a gaban ofishin gwamnati

A yau Litinin, ‘yan sanda a Nairobi, babban birnin Kenya sun harba hayaki mai sa hawaye a kokarin tarwatsa mutanen dake zanga-zangar nuna adawa da abinda suka bayyana da jerin sace-sacen masu sukar gwamnati tare da tsare wasu daga cikin masu zanga-zangar

A ‘yan watannin baya-bayan nan an sace gomman ‘yan Kenya, a cewar hukumomi kare hakkin bil adama, wadanda suka zargi hukumomin ‘yan sanda da takwarorinsu na sirri da aikata kamen daya sabawa doka.

KENYA
KENYA

A cewar hukumomin Kenya, gwamnati bata amince ba kuma bata da hannu a kashe-kashe ko satar jama’ar da suka saba ka’idar doka.

Wasu kungiyoyin matasa masu zanga-zanga sun gudanar da maci a tsakiyar birnin Nairobi a yayin da wasu kananan kungiyoyin ke gudanar da zaman dirshan yayin da hayakin barkonon tsohuwa ke yawo a iska. Matasan na rera wakokin kyamar gwamnati, yayin da wasu ke rike da kwalayen dake yin tir da tsare mutane ba bisa ka’ida ba su kuma jami’an ‘yan sanda na sintiri akan dawakai a kusa da wurin.

A cikin masu boren har da wani dan majalisa daga jam’iyyar adawa Okiya Omtatah, wanda shima ke zaman dirshan, inda masu zanga-zangar ke amfani da murtaka-murtakan sarkoki wajen makalkale juna yayin da ‘yan sandan kwantar da tarzoma ke kokarin tarwatsasu.

Jaridar Daily Nation ta kasar Kenya ta bada rahoton cewar an tsare Omtatah da was masu zanga-zanga 10 yayin boren.

Kenya
Kenya

Kwamandan ‘yan sanda na birnin Nairobi Adamson Bungei da kakakin rundunar ‘yan sandan kasar Rosalia Onyango sun ki yin martani ga bukatar kamfanin dillancin labaran Reuters ta yin bayani.

Sace-sacen mutanen ta biyo bayan zanga-zangar nuna kyamar gwamnatin data samo asali a watan Yulin da ya gabata.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG