A jiya Litinin, shugaban ya gana da shugaba Barack Obama a fadarsa ta White House don tattauna irin barazanar da mayakan boko haram suka yi ga kasar da kuma wasu batutuwan.
Mr. Obama ya yaba da zaben da aka yi a shekarar nan a Najeriya wanda ya zamo zaben demokradiyya na fari tun da aka kawo karshen mulkin soja a shekarar aluf dari tara da cisi’in.
Shugaba Obama yace mun ga zaben da aka mika mulki ga wata sabuwar gwamnati cikin kwanciyar hankali, wannan ya tabbatar mana da cewa Najeriya na mutumta demokradiyya.
Shugaban na Amurka ya kara da cewa, ya na da damuwa akan hare-haren ‘yan boko haram ya kuma yi Imani da cewa shugaba Buhari na da kyakyawan shiri akan yadda za a murkushe ‘yan kungiyar da kuma magance rashawa da ta kawo cikas ga cigaban tattalin arzikin Najeriya.
Mr. Obama yace yana fata zasu tattauna akan yadda Amurka da Najeriya zasu hada kai akan batutuwan yaki da ta’addanci.
Wanna ziyarar ta shugaba Buhari zuwa nan birnin Washington it ace ta farko tun bayan da ya fara shugabanci a wata Mayun wannan shekarar, bayan zaben luma da ba kasafai aka taba gani ba a Najeriya.