Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Na Tsokaci Kan Bayyanar Sunayen Matattu a Nade-naden Mukamai


Wasu magoya bayan shugaba Buhari a rike da hotonsa yayin wani gangamin nuna goyon bayansa da aka yi a ranar 11 ga watan Agusta 2017 a Abuja
Wasu magoya bayan shugaba Buhari a rike da hotonsa yayin wani gangamin nuna goyon bayansa da aka yi a ranar 11 ga watan Agusta 2017 a Abuja

'Yan Najeriya na ta tafka muhawara a shafin sada zumunta na Facebook tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin sunayen wadanda za su shugabanci hukumomin gwamnatinsa da zama mambobi, sunayen da suka kasance har da wadanda suka rasu.

‘Yan Najeriya na ci gaba da tsokaci game da nadin wasu mutane matattu da aka yi a nade-naden shugabannin da za su kula da wasu hukumomin gwamnati.

Yayin da wasu ke bayyana ra’ayin cewa hakan ya nuna rashin kwarewa a bangaren gwamnatin ta APC wasu kuwa cewa suke lamarin bai kai ga akai ruwa rana ba domin kuskure kowa na yin shi.

An dai fi yin tsokaci kan wannan batu ne a shafin sada zumunta na Facebook wanda ya mamaye sauran batutuwan da ake tattaunawa a kai.

“Kada masu ganin laifin shugaba Buhari, game da nadin da ya yi wa wadanda suka riga mu gidan gaskiya. su manta da cewa shugaban Muhammadu Buhari, dan adam ne” Inji Aliyu Usman takalafiya daga Birnin Kebbi kamar yadda ya rubuta a shafinmu na Facebook.

“Nada wasu matattu mukamai da Gwamnatin A.P.C karkashin Shugabancin Buhari ta yi, hakan ya kara nuna ma Duniya cewa gwamnatin Buhari ta kidime ta rude. Da fatan Jama'a za su yi mata addu'a domin ta dawo cikin hayya cinta.” Inji Haruna Muh'd Katsina, Shugaban Kungiyar muryar Jama’a.

A karshen makon da ya gataba ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nada shugabannin hukumomin gwamnati 209 da mambobinsu 1,258.

Bayanai sun yi nuni da cewa wadannan nade-nade, sune mafi yawa da shugaban ya yi tun bayan da hau mulki a shekarar 2015.

A ranar Juma’a aka bayyana sunayen a wata rubutacciyar sanarwa da ofishin Sakataren gwamnatin tarayya ya fitar.

“Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da wadannan nade-nade na hukumomin gwamnati a wasu ma’aikatu saboda su cike guraben da ke akwai.” Kamar yadda sanarwar ta nuna.

An jima a nata ta dakon nadin shugabannin hukumomin wadanda masu lura da al’amura suka ce sukan taimaka wajen gudanar da ayyukan hukumomin.

Takkadamar Sunayen Matattu

Sai dai Wata takaddama da ta kunno kai ita ce ta kasancewar sunayen wasu mutane uku a jerin sunayen, wadanda bayanai suka nuna cewa sun mutu.

Jaridun Najeriya da dama sun ruwaito cewa daga cikin sunayen wadanda aka nada har da matattu.

Jaridar Daily Trust a shafin yanar gizonta na ranar Asabar, ta ruwaito cewa an nada Sanata Francis Okpozo wanda ya mutu a ranar 26 ga watan Disambar bara a Birnin Benin, a matsayin shugaban hukumar Nigerian Press Council.

Sannan jaridar ta kara ruwaito cewa an nada Donald Ugbaja wanda ya rasu a watan Nuwamba a matsayin mamba a kwamitin kula na hukumar Consumer Protection Council.

Jaridar Premium Times a shafinta na yanar gizon na ranar Asabar, ta ruwaito cewa, an saka sunan Christopher Utov, a matsayin mamban hukumar bincike kan harkokin tattalin arziki wanda ya rasu a ranar 18 ga watan Maris din wannan shekarar a jihar Benue.

Wasu rahotanni da dama sun bayyana cewa an samu bayyanar sunayen mutane sama da daya a hukumomi daban-daban.

Rahotanni sun ce Fadar shugaban kasar ta ce za a gyara kurakuran da ke jerin sunayen wadanda aka nada.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG