Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Wa Yusuf Muhammadu Buhari Tiyata Bayan Hatsarin Babur


Yusuf Buhari
Yusuf Buhari

Likitoci sun yi ma Yusuf Muhammadu Buhari, dan shugaban Najeriya, tiyata, kuma yana kwance yanzu haka a asibiti yana jinyar raunukan da ya samu a dalilin wani hatsarin da yayi a kan mashin.

Jiya da daddare ne Yusuf Buhari ya yi hatsari kan katon babur, ko mashin, a unguwar Gwarinpa da ke babban birnin tarayya, inda ya samu karaya, ya kuma buga kai ya ji rauni.

Mai taimaklawa shugaban Najeriya a fannin kafofin yada labarai na Intanet, Bashir Ahmad, ya bayyana a shafinsa na twitter cewa Yusuf na ci gaba da samun sauki a bayan wannan tiyata da aka yi masa.

Ya kuma ce shugaba Buhari tare da Uwargidarsa sun bayyana godiya ga 'yan Najeriya a saboda irin addu'o'in da suke yi ma Yusuf, tare da rokon Allah Ya saka musu da alkhairi.

Ga abinda Bashir Ahmad yake fada a shafinsa na Twitter:

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG