Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Amince Sayarwa Najeriya Manyan Jiragen Yaki


Jirgin Saman Yaki
Jirgin Saman Yaki

Jakadan Amurka a Najeriya Ambassador Stuart Symington ya mikawa babban hafsin hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marsha Sadik Abubakar takardan amincewar Amurka na sayarwa Najeriya manyan jiragen yaki samfurin A29 Super Tucano goma sha biyu.

Da yake mika takardan, jakadan Amurkan yace Amurka kanta ta zaku ta ga an kawo karshen ayyukan ta’addancin Boko Haram a yankin tafkin Chadi. Ya kuma kara da cewar samun wadannan jiragen yaki nan bada dadewa ba zai zama sanadin Boko Haram ta zama tarihi.


Babban hafsin hafsoshin rundunar saman Najeriya, Air Marshal Sadik Abubakar yace samun wadannan manyan jirage zasu baiwa mayakan saman kwarin gwiwa a yaki da ta’addancin Boko Haram. Yace jiragen suna da kayan zamanin da jiragen na yanzu basu dasu.


Air Marshal Ola Tocombo Ade Sanya, wanda shine darektan watsa labarai a helkwatan sojojin saman Najeriya, ya bayyana yanda za a yi hada hadar wadannan jirage. Yace kafin sanya hannu a kan wannan yarjejeniyar, rundunar sojojin saman Najeriya tare da takwarorinta na Amurka zasu yi nazarin yarjejeniyar kuma kafin karshen watan Faburarirun sabuwar shekarar 2018 zasu sanya hannu akai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG