PORT HARCOURT, NIGERIA - Rahotanni daga yankin kudu maso gabashin Najeriya sun nuna cewa ‘yan bindiga sun sace wani basaraken gargajiya mai suna Eze Ambrose Ogbu a yankin Nnewi da ke jihar Ebonyi bayan da suka kutsa fadarsa a wannan makon.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce ta baza jami’anta don ganin an ceto shi, a ta bakin Aliyu Garba kwamishinan ‘yan sandan jihar. Ya kara da cewa sun kaddamar da aikin sintiri na sirri musamman a kan ruwayen yankin don ganin an ceto basaraken lafiya.
Rashin tsaro a yankin kudu maso gabashin Najeriya na ci gaba da gallabar jama’a inda wasu lokutan bayan an sace mutun sai a fille masa kai.
An dai sha zargin kungiyar IPOB da ke rajin ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biafra da hannu a kisan gillar da ake yi a yankin.
Barry Hope, mazaunin yankin ne, ya ce lamarin tabarbarewa tsaro abin tsoro ne a yankin Naija Delta, ya kuma yi kira ga hukumomi da su kara kaimi wajen inganta tsaro.
Shi ko Daniel Ogochukwu cewa ya yi lamarin ya tsananta matuka, babu wurin tsira. Ana sace mutane, a biya kudin fansa amma kuma a kashe su daga baya.
Saurari cikakken rahoton Lamido Abubakar.