WASHINGTON, D. C. - Maharan sun kai harin ne kafin wayewar gari tare da kona gidaje a garin Mamfe, kamar yadda shugaban hukumar da ke kewayen Manyu ya bayyana.
Garin na Mamfe da ke yankin Kudu maso Yamma na Kamaru bai wuce kilomita 50 daga kan iyaka da Najeriya ba.
Jami’in hukumar Viang Mekala ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa mutane bakwai na kwance a asibiti kuma jami’an tsaro na gudanar da bincike a yankin.
"An shawo kan lamarin kuma bai kamata jama'a su firgita ba," in ji shi.
Tun a shekarar 2017 ne 'yan aware a yankunan kasar Kamaru masu amfani da turancin Ingilishi suka fara fafatawa don kafa kasa mai cin gashin kanta mai suna Ambazonia.
Kungiyoyin da ke dauke da makamai su kan kai hare-hare da yin kashe-kashe a yankunan Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Yamma na kasar da ta fi yawan masu magana da harshen Faransanci.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin na ranar Litinin.
Dandalin Mu Tattauna