Batun yin kaura ta barauniyar hanya abu ne da ya zama ruwan dare a tsakanin al’ummar Najeriya da ma wasu kasashen nahiyar Afrika, duk da cewa akwai masu yin kaura bisa ka’ida don neman rayuwa mai inganci a kasashen Turai da na Larabawa, in ji masana a fannin.
A baya-bayan nan matsalar ta kara tsanani ganin yadda alkaluma suka yi nuni da cewa akalla ‘yan Najeriya miliyan daya da dubu dari uku ke fuskantar kalubalen yin kaura ba bisa ka’ida ba a fadin duniya, kamar yadda kuma adadin ya kasance daidai da na ‘yan gudun hijira a cikin kasar a cewar ACG Ngozi Odigbo, wata babbar jami’ar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya.
Kazalika, rahotannin sun yi nuni da cewa babu wata kasa a nahiyar Afirka, in banda Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da Somaliya da ke fuskantar kalubale dabam-dabam masu tsanani ta fuskar yin kaura kamar Najeriya, kasar da ke fama da masu gudun hijira a cikin gida, safarar ‘yan kasar zuwa waje, shigowar bakin haure da kuma ficewar ‘yan kasar zuwa kasashen waje don neman rayuwa mai ingancı.
Mal. Bulama Bukarti, babban mai nazari a cibiyar Tony Blair da ke birnin Landan, yace dalilai da dama ne ke haddasa ci gaba da ganin matsalar kaura ba bisa ka’ida ba, ciki har da rashin aikin yi, rashin tsaro, da rasin damar karo ilimi, da dai sauransu.
Shi kuma mazaunin kasar Ingila kuma mai tamaka wa ‘yan gudun hijira a kasar su sami takardun zama, Ahmed Mohammad, ya ce abubuwa da yawa sun canja yanzu ba kamar a baya ba, ya kuma kara da jan hankali game da illar yin kaura ta barauniyar hanya.
A wani bangare kuwa, babban jami’’i a hukumar kare hakkin bil’adama ta Najeriya Barrista D.S Bobbo, yace kamata ya yi a duba bangarorin yin kaura biyu, wato na masu shigowa cikin kasar da masu ficewa daga kasar, sai kuma kawar da matsalar cin hanci da rashawa bayan daukar matakan da suka dace daga gwamnati doń rage matsalar zaman kashe wando tsakanin matasa.
A game da neman mafita, Bulama Bukarti ya ce kamata ya yi gwamnati ta mangance matsalar rashin aikin yi, rashin tsaro, ilollin sauyin yanayi, da dai sauransu.
Alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa a halin yanzu akwai sama da mutane miliyan 3 da ke gudun hijira a cikin Najeriya, sai miliyan 1.7 da ba su dawo gida ba wasu kuma na gudun hijira a wasu kasashe, sai kuma ‘yan gudun hijira da masu neman mafaka a Najeriya su dubu 74.
Kazalika, sama da 'yan gudun hijira dubu 300 ‘yan Najeriya ne ke a makwabtan kasashen Nijar, Chadi, da Kamaru suma suna jira a dawo da su gida.
Duba da yadda al’amuran gudun hijira ke sauyawa gwamnatin Najeriya na kara fitar da sabbin tsare-tsare wajen daidaitawa da kula da bakin haure.
Saurari rahoton Halima Abdulrauf:
Dandalin Mu Tattauna