WASHINGTON, D.C. - Harin ya auku ne a ranar Alhamis, kamar yadda mazauna garin da wani wakilin kamfanin dillancin labarai na Reuters suka bayyana.
'Yan aware wadanda ba su da yawa masu magana da harshen turancin Ingilishi na kasar Kamaru, sun dade suna fafutukar ganin sun kafa kasa mai cin gashin kanta mai suna Ambazonia tun a shekarar 2017.
Sukan kai hare-hare, garkuwa da mutane da kashe-kashe a yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma na kasar.
Mazauna yankin sun ce maharan sun iso ne da sanyin safiya, a cikin satin ne da aka bude makarantu bayan hutun bazara, kuma an kashe mutane da dama.
A shekarar 2017 ne masu ta da kayar baya suka fara fafatawa da sojojin Kamaru bayan da aka murkushe masu zanga-zangar farar hula da ke neman karin wakilcin tsirarun masu magana da harshen Ingilishi na kasar Faransa.
Galibi ana kai wa makarantu hare-hare lamarin da ke sa tsarin ilimi na Kamaru ya yke tabarbarewa.
Kamar a shekarun baya, masu neman ballewa daga kasar sun ba da umarnin kada a bude makarantu tare da sanya dokar hana fita.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna