Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Dan Jarida A Kasar Kamaru


FILE - Martinez Zogo wani dan jarida da aka kashe a Yaounde, Jan. 23, 2023.
FILE - Martinez Zogo wani dan jarida da aka kashe a Yaounde, Jan. 23, 2023.

‘Yan bindiga sun harbe wani dan jarida da yammacin ranar Lahadi a Bamenda, birnin da ke yankin arewa maso yammacin kasar Kamaru mai fama da rikici, in ji kungiyar ‘yan jarida a kasar, a kalla an kashe ma’aikatan yada labarai uku a kasar cikin wannan shekara.

Anye Nde Nsoh, babban jami’in ofishin jaridar the Advocate na yankin yamma da arewa maso yamma, yana cikin wata mashaya a unguwar Ntarikon da ke garin Bamenda, lokacin da wasu da ba a san ko su waye ba suka bude masa wuta, in ji abokin aikinsa Melanie Ndefru, wadda ke kusa da wurin da harin ya faru.

A farkon wannan shekara, an kashe wani dan jarida da wani mai gabatar da shirin rediyo a wasu hare-hare guda biyu a Yaounde babban birnin kasar, lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa game da yanayin kafafen yada labarai.

Kungiyar ‘yan jarida masu magana da Ingilishi ta Kamaru (CAMASEJ) ta tabbatar da mutuwar Nsoh tare da yin kira da a gudanar da bincike.

Shugaban CAMASEJ Jude Viban ya ce "Wannan harin da aka kaiwa dan jaridar yana da ga cikin hare-hare masu yawa da ake kaiwa. Rikicin da aka dade ana fama da shi a yankunan arewa maso yamma da kudu maso yamma ya jefa 'yan jarida cikin hadari."

Mai magana da yawun hukumomin yankin ya ce ba su da labarin harin. Kawo yanzu dai babu wanda ya dau alhakin harin.

Mutuwar Nsoh ta zo ne a daidai lokacin da ake gwabza fada tsakanin hukumomin Kamaru da wasu kungiyoyin ‘yan aware a yankunan masu amfani da turancin Ingilishi, wanda ya rikide zuwa tashin hankali a shekarar 2017.

Dubban mutane ne aka kashe a fadan da aka gwabza tsakanin ‘yan aware masu dauke da makamai da dakarun gwamnati, tare da cin zarafi daga bangarorin biyu.

XS
SM
MD
LG