Hare-haren 'yan-bindiga a wasu yankunan Kaduna dai ba bakon abu ba ne amma kuma wannan ne karon farko da 'yan-bindiga ke neman maida babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria tarkon mutuwa abin da al'umar yankin ke cewa babbar barazana ce ga Arewa.
Daya daga cikin jagororin 'yan-sa-kai da ke sintiri tsakanin kwanar Farakwai zuwa Zaria, wanda ya nemi mu sakaya sunansa ya shaidawa Muryar Amurka cewa al'umar yankin na cikin matukar damuwa.
"Gaskiya abubuwan da ke faruwa a hanyar Kaduna zuwa Zaria, sai dai mu ce inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un."
Tuni dai kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya tabbarwa Muryar Amurka abin da ke faruwa amma ya ce ana daukar matakai dakile barazanar.
Karin bayani akan: Kaduna, Samuel Aruwan, Muryar Amurka, 'yan bindiga, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Masana harkokin tsaro dai na ganin idan ba an gaggauta daukar mataki ba, lalle tare hanyar Kaduna zuwa Zaria zai iya durkusar da kasuwanci da noma a Arewa, in ji Manjo Mohammed Bashir Shu'aibu Galma mai ritaya.
A 'yan watanni baya, hanyzar Abuja zuwa Kaduna ce ta zama tarkon mutuwa, lamarin da ya matafiya da dama ke bin hanyar jirgin kasa maimakon tafiya a mota.
Daruruwan mutane aka sace a kan wannan hanya kana wasu da dama sun rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa a yankin.
Saurare cikakken rahoton cikin sauti: