Gwamnan jihar ya yi alkawarin tura jami’an tsaro da dama jiya Lahadi, bayanda mahara suka kashe mutum 88 a jihar Kebbi da ke Najeriya a ranar Alhamis da ta gabata, yayinda matsalar rashin tsaro ta ke cigaba da yaduwa kamar wutar daji batare da daukan mataki ba a arewa maso yammacin kasar.
Maharan sun kai hari kauyuka 8, suka kashe mutane kuma suka saka mazauna tserewa. yan sanda sun ce mutane 88 suka mutu. An dai fara samun bayanai ne a ranar Asabar da ta gabata.
Karin bayani akan: jihar Kebbi, Zamfara, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu ya fada jiya Lahadi cewa maharan sun shigo ne daga jihohin Zamfara da Neja makwabtan jihar, wanda suka sace shanu da lalata amfanin gona.
A yan shekarun baya bayan nan yan bindiga suna ta kai hare-hare kan al’ummomi da ke yankin, wanda ya tilastawa dubban mutane da ke zaune a kan iyakar arewacin Najeriya zuwa jamhuriyar Nijar.