Maharan sun kai harin ne a daren Juma’a, inda suka kashe mazauna kauyen Solhan a lardin Yagha, da ke iyaka da Nijar. Sun kuma kone gidaje da kasuwar, in ji gwamnatin a cikin sanarwar.
Gwammnati ta ayyana zaman makoki na tsawon sa'oi 72, tare da bayyana maharan a matsayin 'yan ta'adda, koda yake babu wata kungiya da ta dauki alhakin hakan. Wasu mazauna yankin 40 kuma sun ji rauni, kamar yadda kakakin gwamnatin Ousseni Tamboura ya fada daga baya ga manema labarai.
Hare-haren na masu kishin Islama dake da alaka da kungiyar al-Qaida da kungiyoyin Islama a yankin Sahel na Afirka ta Yamma ya tashi sosai tun daga farkon wannan shekarar, musamman a Burkina Faso, Mali da Nijar, inda ya fi shafan.