Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Na Kafa Sansanoni A Jihar Kano, Ganduje Ya Nemi Agaji


Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano
Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi korafin cewa ‘yan bindiga na nan suna kafa sansanoni a dazukan jihar, inda su ke kokarin maidawa maboyarsu.

A yayin da yake jawabi sa’adda ya ziyarci shelkwatar tsaron Najeriya da ke Abuja, gwamna Ganduje ya ce ‘yan bindiga suna kwarara tare da kafa sansanoni a dajin Falgore da ke cikin jihar, kuma ba mamaki suna yunkurin kai farmaki ne ga jama’ar jihar.

Ya ce ya ziyarci shelkwatar tsaron ne domin neman agaji da taimako, tun kafin lamarin ya baci, har ‘yan bindigar su soma aiwatar da kudurinsu.

Gwamnan ya tattauna da Babban Hafsan Tsaro Janar Lucky Irabor, da babban hafsan sojin kasa Manjo Janar Farouk Yahaya, da na sojin sama Oladayo Amao da kuma na sojin ruwa Vice Admiral A.Z. Gambo.

Ya fada a lokacin ganawar cewa, “na zo ne domin neman agaji da taimakon rundunar sojin Najeriya domin wanzar da zama lafiya a jihar Kano.”

“Muna gina gidaje da asibitoci ga makiyaya a dajin na Falgore, muna bukatar sojoji su soma gudanar da ayukan sintiri a dajin,” in ji Ganduje.

Gwamnan ya bukaci rundunar sojin da ta gaggauta kammala aikin da ta tsara na kafa sansanin horarwa a dajin, ta yadda za su mamaye dajin.

Haka kuma Ganduje ya yi amfani da damar ziyarar, ya jajanta tare da yin ta’aziyya akan rasuwar tsohon hafsan sojin Janar Ibrahim Attahiru da wasu jami’ai 10 a hatsarin jirgin sama, lamarin da ya ce babban rashi ne ga kasa baki daya.

Da yake mai da martani, hafsan sojin kasa Manjo Janar Farouk Yahaya, ya ce rundunar sojin ta sabunta kudurin ta na magance matsalar tsaro a duk fadin kasar.

Yahaya ya kuma yi alkawarin cewa zai kai ziyara a dajin na Falgore, domin duba yadda sojiji za su yi aiki a wuraren da aka gina musu a dajin na Falgore.

XS
SM
MD
LG