Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Baba Alkali, ya tabbatar da cewa rashin fahimta da kuma takaddama, har ma da kiyayya da juna tsakanin hukumomin tsaron kasar, na haifar da mummunan lahani ga tsaron cikin gida na kasar.
Yayin da yake jawabi a wajen bude wani babban taron fadakarwa akan karfafa hadin gwiwa da aiki tare tsakanin ma’aikatar lamurran ‘yan sanda da sauran hukumomi, Alkali ya ce rashin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro kamar soji, ‘yan sanda da kuma jami’an tsaron farin kaya wato DSS, na ci gaba da damun ‘yan Najeriya da dama tsawon shekaru.
To sai dai ya ce wannan matsalar kuma ba ta kebanta kawai a Najeriya ba, ta sha fi kasashe da dama a duniya.
Babban Sufeton ‘yan sandan ya ce “wannan takaddama tsakanin hukumomin tsaro, tana salwantar da kudaden gwamnati a banza, tana kuma kawo maimaita ayuka da zargin juna, da kuma shiga hurumin aiki na juna a tsakanin hukumomin tsaron.”
Shi ma da ya ke jawabi a wajen taron, Ministan lamurran ‘yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi, ya ce tura ta soma kai bango akan aikata manyan laifukan ta da zaune tsaye, da kuma fafutukar ballewa daga kasa a wasu sassan kasar.
Karin bayani akan: DSS, Zamfara, Katsina, Sokoto, Muhammad Maigari Dingyadi, Usman Baba Alkali, tsaro, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Ya ce wadannan munanan laifukan sun hada har da kai hare-hare akan hukumomi da jami’an tsaro da saura Abubuwan gwamnati a kasar nan.
Dingyadi ya ce muddin kuma ana son shawo kan wannan matsalar, to wajibi ne a sami fahimta, aminci da aiki tare tsakanin rundunar ‘yan sanda da ke da alhakin tabbatar da tsaron cikin gida, da kuma sauran hukumomin tsaro.
Masu fashin baki a Najeriya sun dade suna bayyana ra’ayin cewa rashin jituwa da aiki tare tsakanin hukumomin tsaro, na daga cikin dalilan da ke kawo tarnaki a yaki da matsalar tsaro a kasar.
Ko baya ga takaddama tsakanin rundunar ‘ya sanda da soji, haka ma manazarta sun lura da yadda a can baya ake fuskantar matsalar rashin aiki tare ko a cikin rundunar soji, tsakanin sojin sama da na kasa, wadda ta haifar da rashin tasirin hare-haren da aka kai da nufin murkushe ‘yan bindiga a jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto a Arewa maso yammacin Najeriya.