Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 26 ga watan Yuni na ko wace shekara, a matsayin ranar yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi don kawo karshen tu'ammali da miyagun kwayoyi a duniya baki daya.
Taken ranar na wannan shekarar shi ne 'Share Facts On Drugs, Save Lives' wato bada labarun gaskiya kan illar kwaya, ceton rayuka ne.
A kokarinsa na yaki da shan miyagun kwayoyi, shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na Najeriya Brig. Gen. Buba Marwa ya ce hukumar za ta yi amfani da wadannan kwanaki tare da hada karfi da karfe da hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yaki da miyagun kwayoyi (UNODC), kungiyoyi masu zaman kansu, gidajen yada labaru da masu ruwa da tsaki don wayar da kan jama'a game da irin illolin dake tattare da shan miyagun kwayoyi musamman a Najeriya.
Janaral Buba Marwa ya ce duk da cewa hukumar na aiki tukuru don kawo karshen tu'ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya, aikin ba nata bane ita kadai iyaye, sarakunan gargajiya da malaman addini ma sai sun bada ta su gudumawar.
Marwa ya kuma kara da cewa abin takaici ne a ce Najeriya na cikin kasashen dake kan gaba wajen tu'ammali da miyagun kwayoyi.
A nasa bangaren shugaban hukumar na birnin tarayya Abuja Muhammad Malami Sokoto ya ce fatauci da shan miyagun kwayoyi a Abuja abu ne da ya dauki sabon salo.
Ana danganta abinda ke ta'azzara miyagun ayyuka har ma da ta'adanci da shan miyagun kwayoyi.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hauwa Umar: