Shugaban hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Abdulrasheed Bawa, ya ce suna kan gudanar da bincike kan tsohon Gwaman jihar Legas Ahmed Bola Tinubu.
Bawa ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Thisday wacce aka wallafa a ranar Lahadi.
"Ana kan gudanar da bincike, ka san idan kana bincike kan al’amari irin wannan, ba a kammalawa cikin kwana daya, akwai dubban bincike da muke yi kusan a kullum" Bawa ya ce.
Kalaman shugaban na EFCC na zuwa ne a lokacin da aka tambaye shi inda aka kwana dangane da wasikar da EFCC ta taba aikawa Tinubu kan ya bayyana kadarorin da ya mallaka.
Sai dai yayin hirar, Bawa ya ce, hukumar ta EFCC sai ta tantance kowane irin korafi da aka aika mata kafin ta dauki mataki.
"Muna da abin da muke kira kwamitin tantancewa a duk rassan ofisoshinmu, shugaban wannan shiyya da shugaban kwamitin, su suke da hurumin su tantance kowane irin korafi." Bawa ya ce.
Shi dai Tinubu jigo ne babba a jam'iyya mai mulki ta APC, ko da yake, rahotannin baya-bayan nan na cewa akwai 'yar tsama a tsakaninsa da fadar gwamnati, rahotonni da fadar ta Buhari musanta.
An dai taba zargin Tinubu da kamfanin Alpha-Beta da yin sama da fadi da biliyoyin nairori, tare da kaucewa biyan haraji da kuma halalta kudaden haram, zargin da kamfanin ya musanta.
Alpha-Beta kamfani ne da gwamnatin jihar Legas ta dauki hayarsa don ya rika bibiya tare da tattaro alkaluman kudaden harajin jihar ta Legas.
Rahotannin sun ce kaso mafi tsoka na kamfanin mallakar Tinubu ne, wanda ake biya kwamishon idan ya taimaka wajen tattara alkaluman harajin jihar.
Tinubu ya mulki jihar ta Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya a tsakanin 1999 zuwa 2007.
Tsohon shugaban kamfanin na Alpha-Beta, Mr. Dapo Apara da aka sallama a baya ne ya fara kwarmata bayanan cewa kamfanin na da hannu dumu-dumu wajen karkata akalar kudaden harajin jihar tare da kaucewa biyan haraji.
Sai dai wata sanarwa da kamfanin ya fitar a baya ya musanta zargin Mr. Apara, inda ya ce zafin korarsa da aka yi a aiki ne saboda an same shi da handame kudaden kamfanin, ya sa yake wadannan zarge-zarge.