Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Jakadar Najeriya Ke Yunkurin Mayar Da Yan Najeriya Mazaunan Ukraine Gida


Yan Najeriya a Ukraine
Yan Najeriya a Ukraine

A cikin wate hira ta musaman da Muryar Amurka, Jakadiyar Najeriya a Romania, Safiya Ahmad Nuhu, ta shaidawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa sama da 'yan Najeriya 900 zuwa 100 ne suka isa Bucharest daga Ukraine

Haka kuma akwai wasu da yawa a cikin motocin bas da ke fitowa daga wuraren shiga daban-daban tun daga juma’a, kuma har yanzu suna kan shigowa, kuma yawanci dalibai ne.

Suna kuma karban su da hannu biyo, a basu, ruwa abinci, da masauki har wani sa’I har da katin waya don su sami su kira gida. Su ka ma a bangaren su na ofishin jakadanci, dama akwai kudin da aka ware na mussaman da aka bayar saboda a tarye su da shi sannan a maryar da su Najeriya.

Ta kara da cewa, hukumomin Romania sun taimaka matuka wajen hada kai, shiri da taimako. "Ba ma gwamnati kadai ba har ma da daidaikun mutane, kungiyoyi, jami'o'i, masu zaman kansu duk sun taimaka sosai wajen ba da taimako.

Ta ce za a fara mayar da su gida idan jirgin ya isa Bucharest.

Ta kuma bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ce ta dauki nauyin jigilar 'yan Najeriyan da ke bukatar komawa.

Saurari cikakkakkiyar hirar cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:27 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG