Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Weah Ya Sha Kaye A Zaben Shugaban Kasar Laberiya


George Weah Da Joseph Boakai
George Weah Da Joseph Boakai

Shugaba George Weah na Laberiya ya sha kaye a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Talata, bayan da sakamakon farko ya nuna cewa abokin hamayyarsa Joseph Boakai ne ke kan gaba da mafi rinjayen kuri'un da aka kada.

Jami'an zaben na kasar sun riga sun tantance 99.58% na kuri'un, inda Boakai ke kan gaba da 50.89% yayin da Weah ya samu kashi 49.11%.

Ya zuwa yanzu Boakai ya samu kuri’u 814,212 daga cikin kuri’u 1,625,684 da ake da su, sabanin kuri’u 785,778 da Weah na jam’iyyar Coalition for Democratic Change ya samu. Jama’ar da suka kada kuri’a a zaben sun kai kashi 65.77 cikin 100.

Rahotanni sun ce tuni shugaban na Laberiya ya amince da shan kaye. ” na yi magana da zababben shugaban kasa Joseph Boakai domin taya shi murnar nasarar da ya samu,” in ji George Weah a gidan rediyon kasar. “Ina kira gare ku (magoya bayansa) da ku yi koyi da ni, ku amince da sakamakon zaben.

Weah ya ce jam’iyyar su ta CDC ta sha kaye amma, kasar sa ta Liberiya ta yi nasara, domin magana ce ta haɗin kan kasa ba ta mutum daya ba.

Idan za a iya tunawa dai, da irin wannan sakamakon ne George Weah ya doke Joseph Boakai a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Laberiya da ya gudana shekaru shida da suka gabata.

Shugabannin kasashe sun fara aikewa da sakwannin taya murna ga zababben shugaban Liberia Joseph Boakai, cikin su har da shugaba Joe Biden na Amurka da Bola Ahmed Tinubu na Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG