Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

George Weah Ya Zama Sabon Shugaban Kasar Liberia


Sabon Shugaban Liberia George Weah
Sabon Shugaban Liberia George Weah

Duk da yake bai da sanayyar salon shugabanci don bai taba shugabancin a siyasance ba; don haka ba a san kamun ludayinsa ba - don kuwa ba a taba gani ba - duk da haka, George Weah ya zama Shugaban Kasar Laiberiya (Liberia) saboda tsabar shaharar da ya yi wajen wasan kallon kafa, abin da ya sa ya yi farin jini.

An ayyana tsohon shaharren dan wasan kwallon kafar nan George Weah, a matsayin wanda ya ci zaben Shugaban kasar Liberia.

Hukumar zaben kasar ta fadi jiya Alhamis cewa Weah ya ci kashi 61.5 % na adadin kuri’un da aka kada sannan ya ci 14 daga cikin Kananan Hukumomin Liberia 15.

Weah ya kara da Mataimakin Shugaban kasa Joseph Boakai don maye gurbin Shugaba Ellen Johnson Sirleaf, wadda ke sauka bayan wa’adi na biyu, wanda shi ne na karshe bisa ga tanajin kundin tsarin mulkin kasar Liberia.

Hukumar zaben ta ce an fito zaben da kashi 56% - wato kasa da fitowar da aka yi ran 10 ga watan Oktoba lokacin da Boakai da Weah su ka yi kunnen doki, wanda ya kai ga zagaye na biyu.

Masu saka ido sun ce zan tsara tasoshin zaben fiye da yadda aka yi a zaben na watan Oktoba, kuma matsaloli kalilan aka ba da rahoton gamuwa da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG