Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majilisar Wakilai A Liberia Ta Zabi Sabon Shugaba

Ivory Coast's President Alassane Ouattara (L), Nigeria's President Goodluck Jonathan (2nd L), Benin's President Thomas Yayi Boni and Liberia President Ellen Johnson Sirleaf (R) are pictured at the 43rd ECOWAS meeting.

Yayin da akakammala shirin bikin mika mulki ga sabuwar gwamnatinkasar Liberia, tuni har majilisar wakilan kasar ta fara aiki bayan ta zabi sabon shugaban.

Yanzu haka dai an kammala shirye-shiryen mika mulki ga zababben sabon shugaban kasar Liberia, George Weah.

A ranar Littinin din nan mai zuwa ne za’a gudanar da wannan bikin. Kuma yanzu haka mataimakin shugaban kasa mai barin gado Joseph Boakai ya mika takardan sa na barin aiki ga wadda zata maye gurbin sa Jewel Howard Taylor.

Haka kuma tuni majilisar ta 54 ta fara aiki, bayan ta zabi Bhofal Chambers a matsayin wanda zai shugabance ta.

Shi dai Chambers dan jamiyyar shugaban kasa mai jiran gado ne, wato Coalition for Democratic Change ta George Weah.

Chambers ya shaidawa Muryar Amurka a hirar su da James Butty cewa majilisar zata baiwa bukatun al’ummar kasa fifiko ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG