Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

George Weah, Zakaran Kwallon Kafa, Ya Zama Sabon Shugaban Liberiya


George Weah, zababben shugaban Liberiya
George Weah, zababben shugaban Liberiya

An ayyana tsohon zakaran kwallon kafa, George Weah, a zaman mutumin da ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa a Liberiya.

Hukumar zaben kasar ta fada yau alhamis cewa Weah ya samu kashi 61 da rabi cikin 100 na kuri'un da aka jefa, kuma ya lashe jihohi 14 daga cikin 15 na kasar ta LIberiya.

Weah yayi takara da mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai domin maye gurbin shugaba Ellen Johnson-Sirleaf, wadda zata sauka a bayan cikar wa'adinta na biyu kan mulki kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

Hukumar zaben ta ce yawan wadanda suka jefa kuri'unsu yayi kasa da kashi 56 cikin 100 idan an kwatanta da wadanda suka jefa kuri'a a zagayen farko na zaben a ranar 10 ga watan Oktoba, inda Weah da Boakai suka zo na daya da na biyu, suka kuma cancanci shiga zaben fitar da gwani a tsakaninsu.

'Yan kallo suka ce an tsara zaben na wannan mako fiye da na watan Oktoba, kuma ba a fuskanci matsaloli da yawa ba.

Wadda ta yi ma George Weah takarar mataimakiyar shugaba ita ce sanata Jewel Howard-Taylor. Ita dai tsohuwar matar tsohon madugun tawaye, kuma shugaban kasa Charles Taylor ne, wanda ya haddasa yakin basasa a Liberiya a shekarar 1989. A yanzu haka yana zaman daurin shekaru 50 a kurkuku a kasar Britaniya a saboda irin rawar da ya taka a munanan abubuwan da suka faru a Saliyo.

Har yanzu Taylor yana da magoya baya a Liberiya, kuma an ce tsohuwar matar tasa ta taimaka wa Weah wajen lashe wasu muhimman jihohi a zagayen farko na zaben.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG