Wasu ‘yan Najeriya karkashin kungiyar Najeriya daya wato 'One Najeriya' sun nemi gaggauta shari’ar Nnamdi Kanu tare da nuna goyon baya da cewa kasar ta ci gaba da zama tsinsiya daya madaurin ki daya.
Augustine Anthony Tobechukwu, daya daga cikin masu zanga-zangar goyon baya ga Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya ya ce mutanen Najeriya a matsayin 'yan kasa daya dunkulalliya za su amfani juna.
Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, dai ya shigo cikin babbar kotun tarayya ne da misalin karfe 10 saura na safiyar Talata inda ya fara gaisawa da tawagar lauyoyinsa da ke samun jagorancin babban lauya mai mukamin SAN, Mike Ozekhome.
A zaman na ranar Talata aka bayyana shi a matsayin sabon jagoran lauyoyin nasa sakamakon yadda gwamnatin tarayya ta kara wasu tuhume-tuhume wanda a yanayin da ake ciki ya kai adadinsu zuwa 15.
Jagorar zaman kotun, mai Shar’ia Binta Nyako ta shigo kotu kan lokaci kafin Nnamdi Kanu ya iso don shari’arsa da ake yi.
A cikin kotu bayan kin amincewa da zama kan sabbin tuhume-tuhume 15 ciki har da wanda gwamnati ta shigar a ranar Litinin, daya daga cikin tawagar lauyoyin Nnamdi Kanu ya ce karin tuhume-tuhume 8 da gwamnatin Najeriya ta yi cikin kasa da sa’o’i 24 kafin zaman bai dace ba.
Ya kara da cewa hakan na nufin gwamnatin kasar na neman hanyoyin ci gaba da tsare wanda yake karewa ba gaira ba dalili kuma ba su dauki hakan da muhimmanci ba.
Sai dai kungiyar one Najeriya karkashin jagorancin, Muhammad Saleh Hassan, da ta gudanar da tattakin lumana don nuna goyon baya ga kasar ta ci gaba da zama tsintsiya daya madaurinki daya a yayin zaman kotun ta bukaci kotu ta gaggauta yin shari’ar a rufe babin wannan al’amari na Nnamdi Kanu.
Kamar yadda aka saba gwamnati ta jibge jami’an tsaro a kan hanyoyin da suka kai ga babbar kotun tarayya dake unguwar Central Area da kewaye.
Kazalika, wasu magoya bayan Nnamdi Kanu dai sun fantsama kan titi don nuna goyon bayansu.
Domin baiwa lauyoyin Nnamdi Kanu damar kara kintsa wa an dage zaman kotun zuwa Laraba.
Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi