Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ohanaeze Ta Lashi Takobin Bin Diddigin Shari’ar Kanu A Kotu


Nnamdi Kanu.
Nnamdi Kanu.

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo, mai rajin kare muradun ’yan kabilar Igbo, ta bayyana shirin ta bin diddigin shari’ar shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu, ta hanyar tura wakilai da za su sa ido kan shari'ar.

Kungiyar dai ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar da kakakin kungiyar, Alex Ogbonnia, ya rattabawa hannun, bayan cimma matsaya a yayin taron majalisar zartarwarta a ranar Lahadi kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar ta ce wakilan bin diddigin da zata tura din za su yi aiki sau-da-kafa da mai ba ta shawara kan harkokin shari’a da kuma wasu fitattun ’yan kabilar ta Igbo.

BORNO: Deputy Governor with Igbo leaders resident in the state
BORNO: Deputy Governor with Igbo leaders resident in the state

Tun ba yau ba ne, kungiyar Ohanaeze Ndigbo ke bayyana damuwarta kan korafe-korafen ’yan kabilar Igbo da suka hada da dattawa da ma matasa kan cewa ba a damawa da su a harkokin Najeriya wanda kungiyar ta bayyana a matsayin kalubale, ban da rikici tsakanin makiyaya da manoman yankunan kudu da kuma sauran batutuwan da suka addabe su.

A yayin bayyana ra’ayinta na bin diddigin shari’ar, Ohanaeze Ndigbo ta yi kira ga matasan yankunan kudu da su kasance masu bin doka da oda kuma su yarda da matakan da shugabanninsu da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin kudu ke dauka kan magance matsalolin da su ke fuskanta cikin ruwan sanyi.

Wasu kungiyoyin Arewacin Najeriya sun yi zargin cewa a yayin da ‘yan kungiyar IPOB ke afkawa hukumomin tsaro a yankunan kudu, shiru aka ji daga bakin kungiyar ta Ohanaeze Ndigbo kan lamarin, har sai da tashe-tashen hankula suka yi kamari sannan gwamnonin kudu maso gabas suka fito suka nisanta kan su da ayyukan kungiyar IPOB, lamarin da ya sa kungiyoyin na Arewa suka bayyana cewa, gwamnonin ke cusawa yan IPOB ra’ayin neman balewa.

XS
SM
MD
LG