Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Yi Zaman Shari'ar Nnamdi Kanu


Zaman sauraren shari'ar Nnamdi Kanu a Babbar Kotun Tarayyar Najeriya a Abuja
Zaman sauraren shari'ar Nnamdi Kanu a Babbar Kotun Tarayyar Najeriya a Abuja

A ranar Litinin aka yi zaman sauraren karar jagoran kungiyar IPOB Nnamdi Kanu a babbar kotun tarayya ta Abuja, amma kuma ba'a je da shi kotun ba.

Hukumar tsaron Najeriya ta farin kaya wato DSS, ta ki gabatar da jagoran kungiyar fafutukar kafa kasar Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu a gaban kotu, a yayin da aka soma zaman ci gaba da sauraren kararsa a gaban babbar kotun tarayya.

Duk da yake ba’a bayyana a inda Kanu yake ba a gaban kotun, to amma kuma a yayin da aka kira karar ta shi, lauyan gwamnati M.B. Abubakar, ya ta’allaka rashin ganin Kanu a kotu ne da “matsalar kayan aiki”.

To amma kuma da aka tunatar da shi cewa yau ne, 26 ga watan Yuli, aka tsaida a matsayin ranar ci gaba da zaman shari’ar, lauyan ya ce a shirye yake da a ci gaba ko da kuwa Kanu baya a kotun, domin kuwa yana da shaidu 3 da za su bayar da shaida.

Babbar Kotun Tarayyar Najeriya a Abuja
Babbar Kotun Tarayyar Najeriya a Abuja

Sai dai kuma lauya Abubakar ya nemi jin ra’ayin kotu akan ko za’a ci gaba da zaman shari’ar, la’akari da cewa babbar kotun ta soma hutunta na shekara.

To sai dai a nashi bangare, lauyan da ke kare Nnamdi Kanu, Ifanyi Ejiofor, ya ce rayuwar wanda yake wakilta na cikin hatsari, domin kuwa ya sami tabbatattun rahotannin da ke cewa an dauke Nnamdi Kanu daga wurin da Kotu ta ba da damar a ajiye shi.

Lauyan ya kara da cewa ya kasa samun damar ganawa da wanda ya ke kariya a cikin kwanaki 10 da suka gabata.

Duk da haka Ejiofor ya ki amincewa da bukatar lauyan gwamnati ta dakatar da ci gaba da zaman shari’ar sakamakon hutun da kotun za ta shiga, yana mai cewa kamata yayi kotu ta ba da dama ta musamman da za su ci gaba da shari’ar saboda muhimmancinta.

To sai dai kuma Alkalin kotun, Mai Shari’a Binta Nyako, ta bayyana damuwa da rashin gabatar da Nnamdi Kanu a gaban kotu, tana mai cewa matakin farko na shari’ar babban laifi shi ne gabatar da wanda ake kara a gaban kotu.

Akan haka ta ce ba yadda za’a yi a ci gaba da zaman shari’ar ba tare da wanda ake kara a gaban kotu ba.

Haka kuma ta bayyana cewa ba ta da hurumin ci gaba da sauraren shari’ar muddin babu umarni na musamman da ya ba ta damar yin haka alhali kotun na cikin hutu.

To amma kuma ta baiwa hukumar DSS umarnin cewa ta ba Nnamdi Kanu damar ganawa da lauyoyinsa.

Haka kuma ta ba da umarnin a gabatar da Kanu a gaban kotu nan da zuwa ranar 21 ga watan Oktoba, wadda ita ce ranar da aka tsayar domin ci gaba da sauraren shari’ar.

Babbar Kotun Tarayyar Najeriya a Abuja
Babbar Kotun Tarayyar Najeriya a Abuja

An girke jami’an tsaro da dama a cikin shirin ko-ta-kwana a harabar kotun, yayin da kuma aka takaita mutanen da suka sami shiga a cikin kotun, ciki har da ‘yan jarida.

To sai dai hakan bai hana wasu magoya bayan Nnamdi Kanu isa a harabar koton ba, inda suke nuna jinjina da goyon bayansu ga shugaban na su.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG