Wannan matashin, wanda ya ki ya fadi sunansa saboda tsoron kada a kai farmaki kan iyalinsa da 'yan'uwansa, yace, “muna da membobi daga Chadi, da Nijar da kuma Kamaru wadanda muke kai mafi yawan hare-harenmu tare da su.”
Wannan ikirari na cewa akwai mayaka 'yan kasashen waje a cikin Boko Haram, idan gaskiya ne, zai nuna yadda kungiyar take kara rikidewa daga yadda aka santa tun da fari ta matasa dauke da adduna, har ta kawo yanzu ga mai amfani da motoci masu sulke, roka, bama-bamai da bindigogi manya domin cimma gurin da ta yhi ikirari na kafa dokar Islama.
Sai dai wannan matashin da sojojin suka gabatar ma 'yan jarida, yace shi manufarsa ba ta addini ba ce duk da kiransa da ake yi da sunan mayakin Islama, domin kuwa a cewarsa shugabanninsu “ba su taba yi musu wa'azi ko da sau daya a kan Muslunci ba.”
Yace ba a ma ambaton sunan Allah a wurin sai “idan abincinmu ya kare a cikin daji. A nan ne shugabanninmu zasu tara mu, su ayyana cewa zamu fita zuwa aikin Allah da Musulunci.”
Ya kara da cewa, “ni ban taba ganin wani abu na addini a abubuwan da muke yi ba. Mu dai kawai muna kashe mutane ne, muna satar kayayyakinsu, muna kuma shan wahala a cikin daji.”
A cikin makon da ya shige, ministan shari'a na Najeriya, Mohammed Adoke, yayi zargin cewa wasu ne daga kasashen waje suke daure ma kungiyar Boko Haram gidni. Ya bayyana wannan a lokacin da yake kare matsayin Najeriya game da hakkin jama'a a gaban majalisar Kare Hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya a Geneva. Bai yi karin haske kan ko su wanene suke tallafa mata ko daure mata gindin ba.