Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Ce Sun Kashe Mayakan Boko Haram 37 a Borno


'Yan jarida na kallonw asu makaman da aka kwace daga hannun mayakan Boko Haram a Maiduguri, 5 Yuni, 2013
'Yan jarida na kallonw asu makaman da aka kwace daga hannun mayakan Boko Haram a Maiduguri, 5 Yuni, 2013

Shiyya ta 7 ta sojojin Najeriya ta ce an kashe mayakan Boko Haram din ne a wasu garuruwan da suka nemi kai farmaki daga ranar lahadi zuwa jiya litinin

Shiyya ta 7 ta sojojin Najeriya mai hedkwata a Maiduguri, ta ce ta kashe mayakan kungiyar Boko Haram su akalla 37 a wasu arangamomin da aka gwabza a wasu garuruwa daga litinin din nan.

Kakakin shiyyar, Kyaftin Aliyu Ibrahim Danja, ya fada cikin wata sanarwa cewa 'yan Boko Haram sun kai farmaki garin Alagarno ranar litinin, inda sojojin shiyyar tare da tallafin mayakan sama, suka gwabza da 'yan bindigar, suka kashe da dama daga cikinsu.

Wasu mayakan na Boko Haram sun tsere suka bar makamai, da nakiyoyi, da motocin akori-kura guda uku, da babura da dama.

Haka kuma, kakakin yace a ranar lahadi, mayakan Boko Haram su kimanin 50 dauke da manyan makamai kirar AK-47, sun tare hanyar Gamboru-Ngala da Dikwa, kusa da kauyen Lougoumani, inda suka kashe mutane 4, ba wai mutane 19 kamar yadda aka yi ta fada da farko ba.

Yace 'yan bindigar sun kuma kona motocin tirela 4 da tankar daukar mai guda 2, sannan suka kwace wata motar akori-kura dauke da kayan abinci suka gudu da ita.

'Yan Boko Haram din sun tare wasu maharba dake komowa daga ta'aziyyar wani dan'uwansu, suka kashe 4 daga cikinsu, suka kona musu mota.

Haruna Dauda ya aiko da cikakken bayani daga Maiduguri.

Sojoji Sun Ce Sun Kashe Mayakan Boko Haram 37 - 1:52
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00
Shiga Kai Tsaye
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG