An bayyana cewa komai tsit, yayin da al'amuran na yau da kullum suka tsaya cik a Damaturu da sauran sassan jihar a sanadin wannan dokar hana yawo.
Motocin 'yan kasuwa da suka saba bi ta cikin Jihar Yobe a tsakanin Maiduguri da Kano, sun kasa wucewa, inda wadanda suka fito daga Kano yawancinsu suka tsaya a Azare a Jihar Bauchi a saboda hana zirga-zirga a cikin jihar ta Yobe.
A jiya jumma'a ne kakakin Bataliyar Zaratan Sojojin Najeriya ta shiyya ta 3, Kyaftin Eli Lazarus, ya bayarda sanarwar kafa wannan dokar hana fita waje, inda yace an fara aiki da wannan doka tun daga lokacin.
Kyaftin Lazarus ya roki jama'a masu bin doka da oda da su kwantar da hankulansu a yayin da bataliyar take ci gaba da kokarin kawar da 'yan bindiga daga wuraren da suka yi tunga.
Jihar Yobe tana daya daga cikin jihohi ukun da aka kafa dokar-ta-baci a yunkurin kawo karshen cin kare babu babbaka da kungiyar Boko Haram take yi a yankin arewa maso gabashin Najeriya.