Wata matar aure mai suna Maryam Grema, ta ce an kama mijinta tu n ranar 19 ga watan Janairu na wannan shekara kuma har yau ba ta sake juin labarinsa ko halin da yake ciki ba. Malama Maryam ta ce an kama mijin tana da cikin wata 6, kuma ga shi har ta haihu watanni 6 da suka shige, babu ko labarin abinda ya samu mijin nata.
Malama Maryam, wadda ta ce har ta kamu da hawan jini, ta ce ta sha yunkurin neman yadda zata ga mijin nata, amma har yanzu watanni 10 da kama shi, ba ta yi nasara ba. Ta roki gwamnati da hukumomin tsaro da su sauke hakkin dake kansu, na bayyana musu inda mazajensu suke da kuma halin da suke ciki kamar yadda dokokin kasa da kuma na da'a suka bukata.
Hajiya Hauwa Bolori kuma ta ce an kama musu 'ya'ya tun ranar 209 ga watan Mayu, kuma har yanzu hukumomi ba su ce musu uffan ba, ba su kuma kyale su sun san halin da suke ciki ba. Ta ce an karkashe wasu a lokacin da aka kama 'ya'yan nasu, kuma ba su san ko sauran su na nan da rai ko a'a ba. ta ce wasu daga cikin iyayen da abin ya shafa ma har sun yi sadaka, bisa kyautata zaton cewa 'ya'yansu dai ba su nan da rai yanzu.
Ga rahoton da Haruna Dauda ya aiko daga Maiduguri kan wannan batun.