Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa dake da sa hannun Lautenan Kanal Mohammed Dole mai magana da yawun kungiyar. Sanarwar ta ce ta gano sansanin 'yan kungiyar ne a kauyen Galandi da Lawanti duk a jihar. Ya ce ranar ashirin da hudu na wannan watan suka gano sansanin. Tare da hadin gwiwar mayakan sama da dakarun kasa suka kai harin da ya hallaka mutanen. Ban da wadanda suka mutu wasu da dama sun raunata lokacin musayar wuta. Haka ma sun lalata motocin akori kura guda bakwai da sojoji suka ce na 'ya'yan kungiyar ne. Sanarwar ta yabawa jama'a game da irin goyon bayan da suke basu. Jami'an tsaro sun cigaba da fafatawa da 'yan kungiyar..
Wannan sanarwar kisan 'yan'yan Boko Haram su saba'in da bakwai ta zo daidai lokacin da jihar Yobe mai makwataka da jihar Borno ke fuskantar karin kai mata hare-hare daga wasu 'yan bindiga da ake zato 'yan kungiyar Boko Haram din ne. Jiya 'yan bindiga suka kai hari kan 'yansanda da wuraren da ake binciken ababen hawa a cikin garin Damaturu babban birnin jihar Yobe lamarin da ya sa aka kafa dokar hana fita ta sa'o'i ashirin da hudu. Kawo yanzu abubuwa sun tsaya cik a garin Damaturu.
Haruna Dauda Biu nada karin bayani.
LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”