WASHINGTON, DC —
Rahotani daga karamar hukumar Kukawa, dake jihar Borno, na nuni da cewa wasu mahara da ake zaton ‘yayan kungiyar Boko Haram,ne sun kai sun kai hari kan mazauna garin inda aka ce sun hallaka mutane da dama kuma suka kona garin.
Wannan harin shine karo na biyu cikin makoni biyu da aka kai kan mazauna wannan gari na Kukawa, maharan dai sun afkawan mutanen garin ne daidai lokaci da suke Sallah.
Wannan hari dai yayi sanadiyar mutuwar mutane dari da goma sha ukku{113}, wanna batu dai na hare hare masamman ma a wannan yanki na shiyar arewa maso gabacin Najeriya, na ci gaba da fadada duk da ummarnin da shugaban kasa ya baiwa hafsoshin kasar da su koma da hedkwatarsu zuwa Maiduguri.