Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaikayi ta Koma Kan Mashekiya


Wata budurwa mai kimanin shekaru 14 ta hallaka kanta a dai-dai lokacin da ta yi kokarin shiga harabar masallacin Juma’a na Aliyu Ibn Abu-Dalib dake daf da shatale-talen Dangi na kan Titin Zaria a birnin Kano.

Lamarin ya faru ne a yayin da ake daf da kamala sallar Tarawi, a mMasallacin inda daruruwan masallata ke gabatar da sallah a cikinsa, wasu mutane da suka ganewa idanunsu sun ce wasu mutane ne suka sauke yarin yar daga cikin wata mota a bakin titi kuma suka bata umarnin shiga harabar Masallacin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano dai ta tabbatar da mutuwar wannan ‘yar kunar bakin wake inda tace wasu mutun biyu su samu raunuka sanadiyar fashewar Bom din da yake jikinta.

Alamarin dai yana zuwa ne kwana daya baya fashewar wasu tagwayen Boma Bomai a Jos fadar Gwamnatin Filato, da kuma garin Potiskum a jihar Yobe wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

XS
SM
MD
LG