Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwanaki Goman Karshen Azumi Nada Falala Matuka


Kwanakin karshe a watan Azumi
Kwanakin karshe a watan Azumi

Goma na marmari goma na wuya koma na daukin sallah asharuwa lafiya. Duk wanda Allah, ya bashi ikon ganin wannan rana ta goman karshen watan azumin wannan shekarar, sai ya gode ma Allah. Kana kuma yayi kokarin amfani da wannanan ranaku wajen bauta ma Allah, fiye da sauran kwanakin wannan watan.

Malan. Isah Jafar, na kungiyar dalibai musulmai ta kasa a jihar Kano, yayi karin haske dangane da falalar da ke tattare a cikin wadannan kwanaki goma da suka rage a cikin watan ramadana. Yayi nuni da cewar Allah, yayi alkawali da duk wanda yasamu dacewa da wannan dare da yafi kowane dare mahimanci a duniya, da cewar Allah, zai amsamasa bukatunsa na alkhairi, wanda ma musamman Allah, ya saukar da aya a cikin Al-Qur’ani wadda take magana akan wannan dare mai albarka. Wannan wata shine watan da Allah, ya saukar da Al-Qur’ani cikinsa.

Akwai bukatar al’umah sutashi tsaye wajen ibadu, a cikin wadannan kwanaki da roka ma kawunansu da ma kasa baki daya zaman lafiya, da ma duk abubuwa da suka dace. Suma wasu bayin Allah, sun nuna nasu fahimtar da wandannan kwanakin da kuma kiraga sauran ‘yan’uwa da su dukufa wajen rokon Allah, a cikin wannan sauran kwanakin. Kana kuma tare da neman Allah, ya karba musu ibadunsu baki daya Allah, yasa suga na shekaru masu zuwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG