Wani jirgin sama da kasar Switzerland kera mai amfani da hasken rana, ya sauka a Hawaii ranar juma’a, bayan da ya kammala wata doguwar tafiyar zagaya duniya da ba a taba yin irinta ba. Tafiyar da yayi ta kan Tekun Pacific itace mafi hatsari.
Jirgin, wanda ya yi tafiya nisan kilomita dubu 35, ya yi wannan shawagi ne ba tare da ko dugon mai ba.
Yanzu matukin Jirgin na Solar “Impulse 2,” Andre Borschberg, ya kafa sabon tarihin wanda ya yi tafiya mafi nisa wacce ta doke tarihin da Ba’amurken nan Steve Fosset ya kafa a baya.
A lokacin yana shawagin, Borchberg ya dan gyan-gyada na mintina 20 a cikin jirgin yayinda jirgin zai sarrafa kansa.
Da farko dai jirgin ya tashi ne daga Nagoya, dake kasar Japan a ranar Litinin bayan yada zango na na babu shiri na tsawon wata guda.
Wasu masana kimiyya ‘yan aksar Switzerland ne suka fara kirkiro wannan jirgi, wato Borschberg da Bertrand Piccard, sun kuma kwashe shekaru 12 ne suna kera wannan jirgi.