Rayuka da dama sun salwanta a arewacin Najeriya, sanadiyar hare haren ‘yan Boko Haram, masamman ma ta hanyar kunar bakin wake lamarin dake ciwa Gwamnatocin arewa tuwo a kwarya.
Gwamnonin sun yi alkawarin taimakawa domin ganin cewa an cimma nasara, sun kuma bukaci jama’a dasu da a ci gaba da adu’ar, Allah ya kawo karshen wannan musiba.
Gwamnan jihar Adamawa, Muhammad Bindo Jibrila, wanda jihar sa ke cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya addaba yace zasu gudanar da wani taro na masamman domin hada karfi da Gwamnatin Tarayya dan gano bakin zaren shawo kan lamarin.
Duk da yake kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin wadannan hare haren na ‘yan kwanakin nan, kungiyoyi da manazarta na ganin cewa dole hukumomin tsaro su sauya salo tare da amfani da naurorin zamani dan samun nasarar waki da masu tada kayar baya.