Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malamai a Jihar Kano: Da Ruwan Ciki Ake Jawo na Rijiya


Malamai
Malamai

Wasu matasa na mika kukansu ga gwamnatin jihar Kano, dangane da halin da suke ciki, tun bayan daukarsu aiki da akayi, ba’a biyasu albashinsuba. Kimanin sama da waatnni bakwai kenan. Sun kuma samu labarin wasu da dama da aka daukesu aiki tare na wasu ma'aikatunni sun samu albashinsu.

Sudai wadannan matasan suna mika kukansu ga gwamnatin jihar Kano, da suyima Allah, su taimaka a basu albashinsu na wadannan watanin da sukayi aiki ba wani albashi, ko abun kyautatawa. A tabakin daya daga cikin masu wannan koken Komorat Yusuf Bashir, yace sun mika wannan koken nasu ta hanyoyi da dama, kuma sunyi tattaki, zuwa gidan gwamnati da duk wuraren da yakamata suje, don su nemi a duba musu damuwarsu.

Amma abun har yanzu ya cittira, don haka sukaga yakamata su kawo kukansu na karshe a wannan gidan radiyon koda Allah, zaisa wannan sakon ya kai ga kunnen mahukunta, don tsakani da Allah, basu da wani kuzari na aiki idan ba an biyasu albashin da suke biba na tsawon watannin hudu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG