Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilin Amurka Na Gabas ta Tsakiya Da Jami'in Falasdinawa Sun Musanya Zafafan Kalamu


Jason Greenblatt, wakilin Amurka na musamman akan harkokin Gabas ta Tsakiya
Jason Greenblatt, wakilin Amurka na musamman akan harkokin Gabas ta Tsakiya

Saeb Erakat jami'in Falasdinawa wanda ya kira Amurka kakakin Yahudawa a shafin wata jarida da ake bugawa a Israila, shi ko Jason Greenblatt ya rubuta a jaridar cewa lokaci ya yi da yakamata a dakile karerayin da Falasdinawa ke ta shatawa shekara da shekaru

Wakili na musamman da Amurka ta nada kan harkokin Gabas ta Tsakiya da wani babban jami’in Falasadinawa, sun yi musayar zafafan kalamai kan yiwuwar samar da zaman Lafiya, tsakanin Isra’ila da Falasadiwa, da kuma rawar da Amurka ke takawa, wajen shiga tsakanin domin sasanta wannan rikici da aka kwashe gwamman shekaru ana yi.

Mai shiga tsakani a bangaren Falasdinawa, Saeb Erakat ne ya fara jefa kalaman a wani rubutu da ya yi a jaridar Haaretz ta Isra’ila, inda ya zargi Amurka da zama “kakakin al’uma” ga Yahudawa, ya kuma caccaki Amurkan kan matakin mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin Kudus a watan da ya gabata, birnin da Israila ke ikrarin shi ne babban birninta, yayin da su ma Falasadinawa ke irin wannan ikrari, ko da nan gaba za a ba su kasa mai cin gashinkanta.

Shi kuwa Jason Greenblatt, wanda shugaba Trump ya nada a matsayin wakili na musamman a Gabas ta Tsakiya, ya maida martani a wani rubutu da ya yi shi ma a jaridar ta Haaretz, yana mai cewa “Amurka ta jima tana nuna kawaici kan irin wadannan kalamai, amma kuma kawar da kai kan kalaman nuna kiyayya da na karya, bai kawo zaman Lafiya ba, kuma ba zai taba kawowa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG