Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Isra'ila Na Kokarin Gyara Yarjejeniyar Nukiliya Da Iran


Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu

Firayim ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya soma wani rangadi zuwa kasashen turai uku a yau litinin, a kokarin shi na neman goyon bayan kasashen kan gyara yarjejeniyar nukiliya ta kasa da kasa da aka kulla da Iran.

Netanyahu ya fara ne da kasar Jamus inda zai tattauna da shugaba Angela Merkel kafin ya karasa a kasashen Birtaniya da Faransa.

Birtaniya da Faransa da Jamus sun shiga yarjejeniyar nukiliya da Iran a shekarar 2015 tare da kasashen Rasha da Chana da Amurka.

Amma a watan da ya gabata ne Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka zata fice daga yarjejeniyar, wacce ya kira mummuna kuma mai cike da bangaranci, a yayin da yake cewa yana son a kara saka ma Iran takunkumi kan shirinta na kera makaman nukiliya, abinda yace yana rikita al’amura a yankin gabasa maso tsakiya.

Sai dai kuma sauran kasashen da ke cikin yarjejeniyar sun nuna shirinsu na ci gaba da zama a cikin ta, inda suka ce tsarin yana tafiya daidai, kamar yadda ake bukata.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG