Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Netanyahu Ya Gana Da Firayi Ministan Birtaniya


Firayi Ministan Birtaniya Theresa May da na Isra'ila Benjamin Netanyahu a London
Firayi Ministan Birtaniya Theresa May da na Isra'ila Benjamin Netanyahu a London

Firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gana da takwaran aikinsa ta Birtaniya Theresa May a yau Laraba a birnin London, yayin da yake kawo karshen rangadin wuni uku da yake yi a Turai da zummar rokon shugabannin kasashen Turai su canza yarjejeniyar kasa da kasa ta nukiliyar Iran.

Netanyahu ya faro rangadin nasa ne daga Jamus a ranar Litinin, inda ya yi kashedi ga shugaban Jamus Angela Merkel cewa shishigi da Iran ke yi a gabas ta tsakiya zai iya haifar da kwararar yan gudun hijira a nahiyar Turai. A jiya Talata ma, firayi ministan Isra'ilan yace bukatarssa ce Iran bata mallaki makamin nukiliya ba.

Netanyahu ya fadawa taron manema labarai na hadin gwuiwa da ya yi da shugaban Faransa Emmanuel Macron a jiya Talata, yana mai cewa, ya dage a kan matsayina na mai adawa da yarjejeniyar nukiliyar, saboda hakan ba zai hana Iran shishigi a yankin ba.

Macron yace Faransa zata ci gaba da yin aiki tare da sauran kasashe, abinda take ganin shine ya fi dacewa wurin sa ido a kan harkokin nukiliyar Iran.

Kamar Netanyahu, shugaban Amurka Donald Trump ya sha sukar yarjejeniyar, yana mai cewa yarjejeniyar ta kyale Iran ta yanda zata iya kera makaman cikin gaggawa da zarar yarjejeniyar ta kare.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG