Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila ta Kai Farmaki a Zirin Gaza


Jiragen saman yakin Isra’ila sun kai hare-hare yau Talata a zirin Gaza, inda suka auna wuraren ‘yan kungiyar mayaka masu zafin kishin addinin Islama.

Hare-haren na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da dakarun tsaron Isra’ila suka ce ‘yan bindiga a Gaza sun harba akalla makamai masu linzame 25 a wurare da dama a kudancin Isra’ila.

Sanarwar dakarun tsaron na Isra’ila ta ce yawancin makaman masu linzame da aka harba, makamin kariya da ake kira Iron Dome ne ya tarbe su, yayinda wasu suka dira a wasu wuraren. Ba a dai sami rahoton wasu sun jikkata ba.

Ana cigaba da samun tashin hankali a bakin iyakar Isra’ila tsawon watanni biyu kenan inda Palasdinawa ke ta zanga-zanga suna neman a maida masu damar komawa kasar da suka gujewa ko aka tilasta masu bari a lokacin da aka kafa Isra’ila a shekarar aluf dari tara da arba’in da takwas. Masu zanga-zangar kuma sun nuna rashin amincewarsu da wani shinge da aka sa a Gaza fiye da shekaru 10, da kuma maida ofishin jakadancin Amurka birnin Kudus daga Tel Aviv.

Wani gungun ‘yan raji, Palasdinawa ya bar Gaza ta kwale-kwale yau Talata don kara nuna kin jinin wannan shingen. Isra’ila ta sanya iyaka akan nisan wurin da jama’a za su iya zuwa da gabar teku, amma ba a san har zuwa ina ‘yan rajin ke shirin kaiwa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG