Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kaddamar Da Sababbin Farmaki A Kan Hamas


Firayi Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Firayi Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu

Ma’aikatar sojin Isra’ila tace jiragen yakinta da jiragenta masu saukar ungulu sun kai wasu sababbin farmaki ta sama a kan Hamas a cikin daren jiya a zirin Gaza, yayin da jirginta mara matuki dake tare makamai masu lizzami ya gano wasu makamai da aka harbo daga yankin Falasdinawa.

Dakarun tsaron Isra’ila sun ce farmakin yana auna wurin kera rokoki da harsasai da kuma tungar sojoji da gine ginen horar dasu.

Bangarorin biyu sun budewa juna wuta tare da kai farmaki a jiya Talata a cikin wani rikici mafi girma tun bayan yakin kwanaki 50 da suka taba yi a cikin shekarar 2014.

"Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya ce, matsanancin lokaci ya wuce a yammacin kogin Jordan da birnin Kudus muasamman da kuma zirin Gaza. Hare hare da Isra’ila ta kaddamar a yau sun yi tsanani a kan zirin Gaza tare da rokoki da kuma jiragen sama. Wadannan hare hare ba na zaman lafiya bane. Koda yake muna son zaman lafiya kuma muna kira ga zaman lafiya. "

Dakarun Isra’ila sun kashe akalla Falasdinawa 115 tun karshen watan Maris, lamarin da ya janyowa sukar lamiri ga yin amfani da karfi. Isra’ila tana zargin kungiyar mayakan Hamas da takala tashin hankali, ta kuma ce ta maida martani ne don kare iyakarta.

Amurka ta kira taron gaggawa a kwamitin sulhu na Majaliusar Dinkin domin tattaunawa a kan sabbin hare haren a kan Isra’ila a zirin Gaza. Anasa ran kwamitin zai yi zama a yau Laraba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG