Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Sabon Firayin MInista a Kasar Jordan


A jiya litinin ne Hani Mulki ya mika takardar yin murabus ga sarki Abdullah.

Sarkin Jordan Abdullah ya nada wani ministan kasar, Omar Razzaz a matsayin firayin minista yayinda aka koma yin zangar-zangar kin jinin gwamnati yau Talata.

Razzaz shine ya maye gurbin Hani Mulki wanda yayi murabus jiya litinin. Mulki dai ya nemi ya dauki matakan tsuke bakin aljihu a kasar.

Dubban ‘yan kasar Jordan sun yi tattaki zuwa ofishin firayin minista mai barin gado, Hani Mulki, da dare har zuwa safiyar yau Talata suna neman gwamnati ta dakatar da hauhawar farashen kayayyaki da kuma shirin kara haraji da masu suka su ka ce mafi akasari matakin zai auna masu matsakaici da karamin karfi ne.

‘Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi arangama da masu zanga-zangar da yammacin ranar Asabar sun kuma harba barkonon tsohuwa don wargaza su daga harabar ofishin firayin ministan. Masu zanga-zangar sun yi ta fadin cewa “jama’a na so su hambarar da wannan gwamnatin."

A safiyar ranar Asabar, sarki Abdullah ya gana da Mulki, da ministocin kasar, da kuma manyan jami’an tsaron kasar. Kamfanin dillancin labaran Jordan na Petra ya ambaci sarkin na cewa "bai kamata ‘yan kasar Jordan su dauki nauyin canje-canjen da aka yi a fannin tattalin arzikin kasar su kadai ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG