Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan Democrats Sun Amince Da Kudirin Dake Dauke Da Sunan Biden


APTOPIX Election 2024 DNC
APTOPIX Election 2024 DNC

A babban taron jam’iyyar Democrats na kasa da aka fara jiya Litinin, wakilai sun amince da takarar jam’iyyar na wannan shekarar ta 2024.

By WILL WEISSERT and ALI SWENSON Associated Press

CHICAGO (AP) —A zahiri, taron jam’iyyar na jiya Litinin da ya gudana a birnin Chicago, bukin share fagen babban taron jam’iyyar na kasa ne inda ‘yan jam’iyyar suka yi ta jadadda manufofofin jam’iyyar a shekaru 4 masu zuwa, duk da cewa da alamu tsohon kudurin jam’iyyar aka yi amfani da shi kasancewar tun bayan da ta ayyana gangamin yakin neman zaben ta a karshen watan jiya, mataimakiyyar shugaban kasa Kamala Harris ta bayyana ‘yan kadan daga cikin manufofin ta na kanta ne kawai la’akari da cewa anyi ta ayyana neman tazarcen shugaba Joe Biden a wa’adi na biyu duk da cewa shugaban ya janye takarar shi wata daya da ya shige.

Kwamitin jam’iyyar Democrats na kasa ya ce takardar mai shafi casa’in (90) yayi bayani mai karfi akan tarihin aikin shugaba Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris tare tsawon lokacin da suka yi aiki tare wanda ke bayyani akan irin kudirin jam’iyyar na irin ci gaban da zamu iya samu a matsayin mu na kasa sannan a matsayin mu na jam’iyya yayin da muke tunkarar shekaru hudu masu zuwa.

kasa Regina Romero ta fadawa wakilan jam’iyyar cewa wakilan sun amince kudurin ne gabanin shugaba Biden ya marawa mataimakiyar shi baya bisa kauna da kuma kishin kasa. Ta kuma sheda cewa a duk da janyewar shi, kwamitin ya shigar da shawarwari daga dukkanin bangarorin jam’iyyar wanda yayi sanadiyyar kudurin jam’iyyar bayyana ra’ayoyin duk alummomin kasar.

Romero ta ce, “Yanzu Kamala ce take jagorantar wannan kudiri.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG