Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harris Ta Samu Goyon Bayan Isassun Wakilan Democrats Domin Tsayawa Takarar Shugaban Kasa – AP


Mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris
Mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris

Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta samu goyon bayan wadatattun wakilan jam’iyyar Democrats domin zama wacce zata kara da Donald Trump 'dan Republican, a cewar binciken da kamfanin dillancin labarai na AP ya gudanar, kasancewar jiga-jigan ‘yan Democrats na mara mata baya.

Hanzarin samun goyon bayan da Harris ke samu wani yunkuri ne da jam’iyyar ke yi na mayar da dambarwar da aka shafe makonni ana yi game da makomar siyasar Biden tare da curewa a wuri guda domin tunkarar aikin kada Trump a zaben da zai gudana nan da kwanakin da basu wuce 100 ba.

Harris
Harris

Nan da nan fitattun jami’an da aka zaba karkashin inuwar Democrat, da shugabanin jam’iyyar da kungiyoyin siyasa suka bayyana goyon bayansu ga Harris a ranar da Biden ya fice daga takarar kuma gangamin yakin neman zabenta ya kafa sabon tarihin tara gudunmowar zaben shugaban kasa cikin sa’o’i 24 a jiya Litinin.

Wakilai daga jihohi da dama sun gana da yammacin jiya Litinin domin jaddada goyon bayansu ga harris, ciki harda Texas da jiharta ta asali California.

Zaben 2024 Democrats
Zaben 2024 Democrats

Zuwa daren Litinin, Harris ta samu goyon bayan fiye da wakilai dubu 1 da 976 da take bukata domin lashe zaben fidda gwanin jam’iyyarta a tashin farko, a cewar kididdigar da kamfanin dillacin labarai na ap ya gudanar. Wakilan da ap din ya tuntuba basu ambaci sunan wani dan takara na daban ba.

Shugaban jam’iyyar Democrat na jihar California Rusty Hicks ya bayyana cewar yayi waya da kaso 75 zuwa 80 cikin 100 na wakilan democrat na jihar California kuma gaba dayansu suna goyon bayan harris.

Democratic National Convention a Philadelphia, na Yuli 26, 2016.
Democratic National Convention a Philadelphia, na Yuli 26, 2016.

Har yanzu wakilan da zasu alarci babban taron jam’iyyar nada damar zaben dan takarar da suke so a taron da zai wakana cikin watan agusta ko kuma idan ‘ya’yan Democrat din suka gudanar da kuri’ar raba gardama ta na’ura gabanin taron da za’a yi a birnin chicago.

A sanarwar data fitar, Harris tayi martani ga kididdigar ta Ap, inda ta bayyana godiya ga shugaba Biden da dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar Democrat da suka mara mata baya, kuma tana fatan mika bukatarsu kai tsaye ga al’ummar Amurka.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG