Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barack Obama Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Kamala Harris

Barrack Obama da Kamala Harris
Barrack Obama da Kamala Harris

A yau Juma’a, tsohon shugaban Amurka Barack Obama da mai dakinsa Michelle sun bayyana goyon bayansu ga Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris a matsayin wacce za ta yi wa jam’iyyar Democrat takarar shugaban kasa.

A yayin da Kamala Harris ke cigaba da samun goyon baya tun bayan da Shugaba Joe Biden ya janye aniyarsa ta sake tsayawa takara sakamakon matsalar da ya hadu da ita yayin mahawara, Obama ya kasance wani jigo a jam’iyyar Democrat da ya bayyana goyon bayansa a karshe.

A wani faifan bidiyon bayyana goyon bayan da suka fitar a yau Juma’a, an ga Obama da mai dakinsa Michelle na bayyana goyon bayansu ga Harris a tare.

Ma’auratan sun kafa tarihi shekaru 16 da suka gabata lokacin da Barack Obama ya zamo bakar fata na farko da aka zaba a matsayin shugaban Amurka.

Idan aka zabe ta, Kamala Harris, wacce asalinta ya shafi bakake da Indiyawan nahiyar Asiya, za ta kasance mace ta farko da za a zaba a matsayin shugabar Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG