Babban taron jam’iyya mai mulki ta Democrat a Amurka, ya shiga yini na biyu a birnin Chicago.
A jerin wadanda aka tsara za su yi jawabi a daren Talata akwai tsohon Shugaba Barack Obama da mai dakinsa Michelle Obama.
Kazalika mijin mataimakiyar Shugaban Amurka Doug Emhoff zai yi magana a gaban taron.
A daren Litinin Shugaba Joe Biden ya gabatar da nasa jawabin a gangamin wanda ake sa ran zai tabbatarwa da Kamala Harris tikitinta na tsaya wa jam’iyyar takara shugaban kasa a zaben 5 ga watan Nuwamba.
Biden ba zai kasance a taron ba a lokacin da Obama zai yi jawabin nasa saboda tuni ya bar birnin na Chicago da ke jihar Illinois bayan gabatar da jawabinsa.
Duba da cewa Biden ya riga ya gabatar da jawabinsa, yanzu hankula za su koma kan Harris da abokin takararta Gwamnan jihar Minnnesota, Tim Walz.
Dandalin Mu Tattauna