Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadiyar Najeriya a Romania Ta Ce Kimanin 'Yan Najeriya 1,000 Suka Isa Bucharest Daga Ukraine


'Yan Najeriya a Ukraine
'Yan Najeriya a Ukraine

Ofishin jakadancin Najeriya a Romania ya karbi 'yan Najeriya kusan dubu daya da suka gudu daga Ukraine, yayin da gwamnatin tarayyar Najeriya ke shirin kwaso 'yan kasarta daga yankin na Turai.

Farmakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine a makon da ya gabata ya sa baki ‘yan kasashen ketare tserewa daga kasar zuwa makwabtan kasashe kamar Poland, Slovakia, Hungary, Romania da sauransu.

Dubban ‘yan Najeriya da galibinsu dalibai ne suka makale a Ukraine, wasu da yawa kuma suka tsallaka zuwa kasashen da ke kusa, ciki har da Romania.

A wata hira da Grace Alheri Abdu ranar Laraba, jakadiyar Najeriya a Romania Safiya Ahmad Nuhu, ta ce takamaimai ba a san yawan ‘yan Najeriya da ke Ukraine ba.

Ta kara da cewa tawagar ‘yan Najeriya dabam daban, da ma wasu dalibai abokansu daga wasu kasashen suka isa Bucharest babban birnin Romania daga sassan iyakokin Ukraine tun daga ranar Juma’a, kuma har yanzu suna kan shiga kasa.

“An bamu umurnin mu karbe su hannu biyu-biyu, mu taimaka musu sannan an tanadi duk abubuwan da zasu bukata kamar ruwa, abinci, da masauki,” a cewar Safiya. Ko da yake ta ce daya daga cikin kalubalen da suke fuskanta shi ne karancin wuraren sauke baki.

Kimanin mutane dari tara zuwa dubu daya ne dai suka isa Romania a cewar jakadiyar, amma ta ce takamaimai ba a san yawansu ba.

Jakadiyar ta kuma fadi cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta kammala shirin kwaso ‘yan kasarta a Romania da sauran kasashen Turai inda suka je, gwamnatin ta dauki nauyin shatar jiragen sama da ake sa ran zasu kwaso sahun farko na ‘yan kasar ranar Alhamis 3 ga watan Maris.

Ta kuma bayyana cewa hukumomin Romania na ba ofishin jakadancin Najeriya a kasar goyon baya tare da taimaka musu sosai.

Saurari cikakkiyar hirar cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:27 0:00

XS
SM
MD
LG