Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Za Ta Daina Aiki Da Matsayin Turai Kan 'Yancin Dan Adam


Kasar Turkiyya ta ce za ta daina aiki da Matsayin Turai kan 'Yancin Dan Adam, a tsawon aikin dokar ta baci na watanni uku, wadda ta kafa don zakulo wadanda su ka shirya juyin mulkin makon jiya, wanda bai yi nasara ba.

Mataimakin Firaministan Turkiyya Numan Kurtulmas, ya ce "Turkiyya za ta dau irin matakin da Faransa ta dauka karkashin babi na 15 na Matsayin Turai din" wanda ya amince kasashen da su ka rattaba hannu akai su jingine amfani da shi a lokacin yaki ko yanayi na rashin tabbas.

"Dokar Ta Bacin za ta bai wa gwamnati damar hukunta wadanda su ka shirya juyin mulkin, da kuma sukunin kakkabe kungiyoyi masu ra'ayin Gulen," abin da kafar labaran Hurriyet ta ambato Kurtulmas na cewa kenan.

Ana kyautata zaton 'yan Majalisar Dokokin kasar Turkiyya za su amince da bukatar Shugaba Erdowan na kafa dokar ta baci ta tsawon watanni uku, matakin da zai kara ba shi damar kakkabe masu adawa da shi, bayan yinkurin juyin mulkin ranar Jumma'ar da ta gabata na hambare shi da gwamnatinsa, wanda bai yi nasara ba.

Erdowan ya yi shelar ayyana dokar ta bacin ne a wani jawabin da aka yada ta gidan talabijin ranar Larabar da ta gabata, bayan wata ganawa da manyan jami'an tsaronsa da Ministoci.

To saidai Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga Erdowan da ya tabbatar cewa bincike da kuma hukunta masu hannu a yinkurin juyin mulkin sun gudana ta yadda jama'a za su cigaba da yin na'am da madahun dimokaradiyya da doka da oda ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG