A yau Laraba wadansu kusoshin jam’iyar da suka yi fice a yakin neman zaben shekara ta dubu biyu da goma sha shida, zasu bayyana dalilan da yasa yafi dacewa da zama shugaban kasa akan da abokiyar takararsa Hillary Clinton.
Gwamnan jihar Indiana, Mike Pence zai yi jawabinsa na farko tun bayan sanar da shi a matsayin abokin takarar Donald Trump. Tsohon kakakin majalisar wakilan Amurka Newt Gingrich, wanda da farko aka yi tunanin shi za a ba matsayin mataimakin shugaban kasa, shima zai yi jawabi yau.
Sauran da zasu yi jawabai sun hada da wadanda suka yi ta sukar tsare tsaren da yake gabatarwa da kuma kalaman batanci da yake amfani da su. Wadanda zasu gabatar da jawaban sun hada da gwamnan jihar Wisconsin Scott Walker, dan majalisar dattijai mai wakiltar jihar Florida Marco Rubio da kuma dan majalisar dattijai mai wakiltar jihar Texas Ted Cruz.
A taron na jiya Talata, ‘yan jam’iyar Republican sun caccaki Clinton, inda suka bayyanata a matsayin ‘yar takarar dake kokarin ci gaba da abinda suka kira tsare tsaren shugaba Barack Obama, yayinda suka kirata makaryaciya wadda ta jefa kasar cikin hadari ta wajen amfani da email din kashin kanta a maimakon na gwamnati.
Kakakin majalisa Paul Ryan ya zargi jam’iyar Democrats da kokarin raba kawunan al’umma.