Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa ta harba makamai masu linzami uku


Koriya Ta Arewa ta harba makamai masu linzami uku, a cewar hukumar sojin Koriya Ta Kudu, mako guda bayan da ta yi barazanar daukar mataki kan shirin Amurka na girke makamin kakkabo makamai masu linzami a Koriya Ta Kudu.

Hafsan Hafsoshin Sojin Koriya Ta Kudu ya fadi a wata takardar bayani cewa an kaddamar da harin ne daga birnin Hwangu na Yammacin kasar da safiyar yau Talata, inda aka harbo su daga nisan kilomita 500 da 600 zuwa kogin Japan. Takardar ta ce Koriya Ta Kudu na nan ta na bin diddigin take-taken Koriya Ta Arewar.

Makon jiya Koriya Ta Arewa ta yi barazanar daukar kwakkwaran mataki bayan da Amurka da Koriya Ta Kudu suka yi shelar shirinsu na girke makamin kariya na 'THAAD' a ruwayen Koriya don taka burki ma Koriya Ta Arewa mai shirin nukiliya da makami mai linzami.

Janar Thomas Vandal, Hafsan sojin Amurka da ke yankin Koriya, ya fadi yayin ayyana shirin a hukumance a birnin Seoul a wannan watan cewa, "Cigaba da kirkiro makami mai linzami da da kuma wasu makamai masu muni da Koriya Ta Arewa ke yi, sabanin abin da ta kan fada ma kasashen duniya, na bukatar kawancenmu ya tabbatar cewa a shirye mu ke mu kare kanmu daga wannan barazanar."

XS
SM
MD
LG